Kaduna: Zabar PDP Asarar Kuri’a Ne – Hunkuyi Dan Takarar Gwamna A NNPP

Dantakarar Gwamnan Jihar Kaduna a inuwar jam’iyyar NNPP Sanata Suleiman Hunkuyi ya janyo hankalin Jama’ar Jihar Kaduna da su guji jefa kuri’unsu wajen Dan takarar da suka san ba zai yi nasara ba, su guji yin zaben tumundare, a ranar 11 ga watan Maris.

Sanata Suleiman Hunkuyi ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, yayin da yake zantawa da manema labarai domin janyo hankalin Al’ummar Jihar Kaduna akan su guji zaben tumundare, kar su yarda su jefa kuri’unsu ga Dan takarar da kowa ya shaida cewa bai da cancanta.

Sanata Hunkuyi ya kara da bayyana cewa, “akan maganar Dan takarar Jam’iyyar PDP, wannan magana na gaban kotu, kuma komai na iya faruwa.”

Ya ci gaba da bayyana cewa, “Tabbas idan aka ci gaba da tafiya a haka, dukkan alamu sun nuna cewa, Jam’iyyar APC mai mulki na iya doke jam’iyyar PDP wajen ganin sun sake lashe zaben gwamna mai zuwa, wanda idan aka bari hakan ya faru, tabbas Al’ummar Jihar Kaduna masu jefa kuri’a ba zasu yafe ma Jam’iyyar PDP ba, a dalilin irin Dan takarar da PDP ta kawo masu, kuma Al’ummar Jihar Kaduna zasu kasance cikin bakin ciki da bacin rai.”

Sanata Suleiman Hunkuyi ya yi kira ga daukacin ‘yan takarar kujerar Gwamnan Jihar Kaduna da su hada kansu waje daya domin ganin basu bar Jam’iyyar APC ta sake darewa bisa karar mulki ba. A cewarsa, suna iya samun hadin kai a cikin awa 24 kamin zabe, domin ganin sun hana Jam’iyyar APC sake kafa gwamnati a Jihar Kaduna.

Daga karshe, Sanata Suleiman Hunkuyi ya bayyana cewa, shi mutum ne mai bin doka da oda, wanda yake kira ga Daukacin Al’ummar Jihar Kaduna su tabbata sun zabi Dan takarar da suke da ra’ayi, domin doka ta baiwa kowa zaben abin da yakeso, batare da musgunawa kowa ba. Inji shi.

Related posts

Leave a Comment