Kada Ka Yi Koyi Da Buhari Wajen Jinkirin Nada Ministoci – Masana Ga Tìnubu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar bayan gudanar da za?en shugaban ?asa a Najeriya , wanda Bola Ahmed Tinubu na jam’iyar APC ya yi nasarar zama shugaban kasar, yanzu kuma hankali ya koma kan irin ?alubalen da ke gaban sabon za?a??en shugaban mai jiran gado.

Masana sun fara bayyana wasu jerin ?alubala da ke kan gaban Tinubu, tare da kira gare shi da kada ya kalli ?angaranci wajen yi wa Najeriya aiki.

BBC ta tattauna da Farfesa Tukur Abdulkadir, wani massanin kimiyar siyasa da ke jami’ar jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, wanda ya ce akwai bu?atar Tinubu ya fara aiki cikin gaggawa ba tare da ?ata lokaci ba.

“Ya kalli abubuwan da suka faru a 2015, kada ya sake ya maimaita abubuwan da Buhari ya yi a baya, kamar jinkiri wajen na?a ministoci da shugabannin hukumomin gwanati.

“Kada ya kalli ?angaranci a shugabancinsa domin kuwa Najeriya zai shugabanta ba wani ?angare ba,” in Farfesa Tukur.

Related posts

Leave a Comment