Hon Lawal Adamu Usman Mr La ya nuna takaici da alhinin sa da jin labarin satar Daliban Bethel Baptist School dake karamar hukumar chikun dake shiyya ta biyun Jihar Kaduna.
A safiyar yau ne aka wayi gari da labarin sace daliban a daren lahadi Wanda haryanzu hukumar makarantar bata fitar da alkaluman Daliban da aka sace ba.
Wasu ruhotanni da kakakin rundunar yan sandan Jihar Kaduna ya Dsp Jalinge ya bayyana cewa ya zuwa yanzu jami’an ‘yan sanda sun kwato dalibai 26 daga cikin Wanda akai Garkuwa dasu Kuma zasu cigaba da kokarin ganin sauran ma sun samu yancinsu.
Mr LA ya shawarci gwamnan Jihar Kaduna da ya zauna yayi karatun ta natsu musamman akan barazanar da yan bindiga kewa fannin ilimi a Jihar Kaduna. Muna nan akayi Garkuwa da daliban kwalejin koyon kimiyar gandun daji Wanda suka kwashe kimanin watanni biyu kamin iyayen su suka amso su, haka ya kara faruwa a jami’ar kudi ta Greenfield, kowa yasan irin wahalar da iyayen yaran Nan suka yi kamin aka sako su bayan ankashe kusan dalibai uku daga cikin su.
Haka ya sake faruwa a Nuhu bamalli polytechnic dake Zariya, Kuma ko a jiya anje asibitin kutare dake Zariya an diba mutane 16.
Babu yadda za ayi gwamnan Jihar Kaduna ya gamsar damu cewa akwai cigaba a fannin tsaro Alhalin Kullum satar mutane da dukiyoyinsu akeyi tamkar Babu gwamnati
