Gombe: Jama’a Sun Amsa Kiran Sabunta Rijistar Zabe

Labarin dake shigo mana daga Jihar Gombe na bayyana cewar gabanin fara harkokin siyasa na shekarar 2023 a Nijeriya jama’a maza da mata na cigaba da yin tururuwa zuwa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar domin yin rijistar katin zabe da ake cigaba da gudanarwa yanzu haka.

Wasu jama’ar da wakilinmu ya zanta su Haruna Mu’azu da Huraira Ahmed da Abubakar Musa Gami da Ahmed Abubakar sun yi kira ga wadanda suka kai munzali yin rijista basu yi rijistar katin zabe ba da cewa suyi kokari suyi kafin lokacin rufe yin rijistar.

Sun ?ara da cewa katin zaben shine makamin su na yin zabe a lokacin zabubbuka, don haka suka yi wannan kira don karfafa gwiwar wadanda basu yi ba su kokarta su yi.

Anashi tsokacin Shugaban sashin ilimantar da masu zabe na hukumar zabe ta kasa reshen jihar Gombe Nuhu Ibrahim yace mutane da dama na fitowa sosai domin yin rijistar, lamarin daya alakanta da taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya gabanin fara rijistar.

Ya kuma ce tuni hukumar ta karbi katunan zabe na din-din din aka fara raba su ga mutane, yana mai cewa katin zabe da hukumar ta karba na mutanen da suka yi rijistar a zango farko da nabbiyu ne na rijistar kuma babu wanda zai karba ma wani kowa da kanshi zai je ofishin hukumar zabe na karamar hukumar da yayi rijistar ya karbi katinshi.

Nuhu Ibrahim yace za a rufe yin rijistar ne a watan Yunin wannan shekara ta 2023 idan Allah ya kaimu.

Da aka tuntubi Kwamishinan hukumar zabe na kasa reshen jihar Gombe Alhaji Ibrahim Umar yace hukumar ta ?aga darajar wasu cibiyoyin za?e zuwa rumfunan zabe a jihar domin rage cinkoso a rumfunan zabe da saukaka wa mutane masu yin tafiya zuwa wurare masu nisa kafin su kada kuri’a.

Kawo yanzu dai mutane na cigaba da karbar katunan su na zabe na din-din da a turance ake cewa Permanent Voters Card,inda Alhaji Ibrahim Umar yace katin zabe baya daina aiki kamar yadda wasu mutane ke cewa.

Related posts

Leave a Comment