Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ?auyen Baka da ke ?aramar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, inda suka kashe uba da ?ansa.
‘Yan fashin wa?anda suka yi wa garin tsinke da farar safiyar yau Asabar, sun je ne domin yin garkuwa da wani manomi da ?ansa, a cewar Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan.
Sanarwar da kwamishinan ya wallafa a Facebook ta ce mutanen sun ?i yarda ‘yan fashin su tafi da su, abin da ya sa suka harbe su nan take.
Sai dai sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wasu ‘yan fashi yayin wasu hare-hare ta sama ?ananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa bayan an gan su tare da shanun da suka sata, a cewar Aruwan.
Matsalar kashe-kashe da ‘yan fashi ke yi a Jihar Kaduna ta zama ruwan dare, duk da cewa gwamnati da jami’an tsaro na cewa suna bakin ?o?arinsu.
A makon da ya wuce ma ‘yan fashin sun kashe mutum 23 a hare-haren da suka kai a ?aramar hukuma uku cikin kwana ?aya.
Mai bai wa Buhari shawara kan tsaro zai gana da gwamnonin arewa maso yamma
Mai bai wa Shugaban Najeriya Buhari shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), zai yi wata ganawa tare da gwamnonin yankin arewa maso yammacin ?asar ranar Litinin.
Wata sanarwa da ofishin tsohon sojan ya fitar ta ce za a yi tattaunawar ce a Kaduna, wadda za ta mayar da hankali kan matsalolin ‘yan fashin daji da suka addabi yankin.
Da ma dai akwai rashin fahimta tsakanin gwamnonin yankin game da hanyoyin shawo kan matsalar, inda wasunsu ke cewa a yi sulhu tare da yi wa miyagun afuwa, wasu kuma ke cewa a ya?e su.
A farkon makon nan ne Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya fa?a wa BBC cewa “idan gwamnatin tarayya ba ta ba mu sojoji na sama da na ?asa ba, an shiga dazukan nan an kashe ‘yan ta’addan nan a lokaci ?aya, to za mu ci gaba da zama cikin matsala”.
Ita kuwa gwamnatin Zamfara na ganin yin sulhu ne mafita, har ma kwamishinan tsaronta ya fa?a ta cikin shirin Ra’ayi Riga na BBC cewa “muna ganin alfanunsa kuma an samu sau?i sosai”.
Kaduna na samun goyon bayan Jihar Neja a wannan batu, yayin da Zamfara da Katsina ke shafi ?aya.
Shi ma Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya tofa albarkacin bakinsa, yana mai sukar El-Rufai game da amfani da ?arfin soja ka?ai a kan ‘yan bindigar.
