‘Yan Siyasa Ne Ke Tafka Magudi Ba Hukumar Mu Ba – INEC

Yayin da ya rage saura kwanaki 60 a yi za?en shugaban ?asa, a ci gaba da shirye-shirye da ta ke yi, Hukumar Za?e ta ?asa (INEC), ta haddada cewa ba ta yin katsalandan wajen shiga har?allar mur?e za?e.

Da ta ke jawabi yayin ganawa da manema labarai da ?ungiyoyin kare ha??i, Kwamishanar INEC ta Tarayya da ke Jihar Ebonyi, Onyeka Ugochi, ta bayyana cewa ‘yan siyasa ne ke shirya magu?in za?e ba hukumar za?e ba.

Ugochi ta ce, “amma da ya ke a wannan za?e mai zuwa INEC ta fito da tsauraran matakan hana magu?in za?e kwata-kwata, musamman ta hanyar amfani da na’urar tantance katin ?an takara, wato BVAS da sauran matakai, babu yadda za a yi ‘yan siyasa su ci kasuwar magu?in za?e.

Daga nan ta yi kira ga kafafen ya?a labarai da ?ungiyoyin kare ha??i su tashi tsaye sosai wajen taya INEC tabbatar da ganin cewa ‘yan siyasa ba su samu wata kafar yin magu?i ba, komai ?an?antar ta.

“Za mu yi dukkan abin da doka ta tanadar da abin da ya wajaba domin mu kauce wa masu so mu ha?a baki da su. Saboda hakan ba zai yiwu mu bada kai borin ‘yan siyasa ya hau ba.

“Kafafen ya?a labarai da ?ungiyoyin kare ha??i ku tashi tsaye a matsayin ku na masu ruwa da tsaki a harkar za?e, ku taya INEC tabbatar da ganin an gudanar da sahihin za?e a ?asar nan. Ku taimaka wajen tabbatar da cewa mun yi abin da doka ta wajibta mana mu yi. Kuma ku taimaka wajen hana masu magu?i su aikata magu?i.”

Daga nan ta sake jan kunne da garga?in cewa masu ?o?arin sayen ?uri’u su sani duk wanda aka kama, to zai yi zaman gidan kurkuku na ahekara ?aya.

Kwanaki 60 kenan kafin a gudanar da za?e, amma tuni har INEC ta jibge jami’an tsaron da su ka ha?a da sojoji, ‘yan sanda, SSS da NSCDC a dukkan ofisoshin hukumar a yankunan da ake ganin akwai barazanar tsaro.

Idan ba a manta ba, a cikin watanni biyu da su ka gabata, an banka wa ofisoshin INEC har bakwai wuta a wasu jihohi na Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas.

Related posts

Leave a Comment