Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga sun fasa gida-gida a yankin Wusasa dake Zariya inda suka sace mutune.
An ruwaito cewa maharan sun farmakin yankin ne mintuna ka?an bayan dare ya raba, inda da farko sun yi awon gaba da mutum 8 kafin suka sake dawowa suka sace Mutum 5.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban yankin Wusasa, Isyaku Yusufu, yace maharan sun shiga gida-gidan wa?an da suka sace yayin da suke bacci.
Kakakin rundunar yan sandan Kaduna, ASP Muhammed Jalige, bai daga kiran wayar salula da aka yi masa ba domin jin halin da ake ciki.
A yan makonnin nan, mazauna Zariya na fama da hare-haren yan bindiga, inda wani lokacin suke tattara matafiya su yi awon gaba da su, ko su shiga gida-gida.
