Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar ?aya daga cikin masu neman kujerar gwamnan jihar karkashin jam’iyyar APC Sani Sha’aban yayi fatali da tsaida ?an takara daya tilo da gwamna El Rufa’i yayi, inda yace za?in El Rufa’i na ?ashin kansa ne ba na jama’a ba.
Sha’aban ya bayyana hakan ne a yayin ganawar da ya yi da manema labarai a Kaduna.
Ya ?ara da cewa jam’iyar APC bata Mutum guda bace ta ‘yan Najeriya ce, kuma jam’iya ce ta ‘yan jihar Kaduna, sannan Deligate ‘yan siyansa ne wa?anda suka bauta wa jam’iya, ba a yi adalci ba ina kira gare su suyi watsi da wannan za?i na El Rufa’i su za?i ?an takarar da ya dace.
Sani Sha’aban ya koka matuka kan yadda ake neman tauye hakkin ‘yan siyasa musamman masu zaben fidda gwani ta hanyar ?a?aba musu ?an takara daga gidan Gwamnati wanda hakan ke nuna rashin adalci ?arara.
Yayi kuma yi kira ga ‘yan siyasa da sauran Al’ummar jihar Kaduna da cewa su guji kuskuren zaben wanda zai koma yana yiwa ubangida biyayya maimakon jama’a.
