Babbar Kotun Koli dake Kaduna ?ar?ashin jagorancin mai Shari’a Daniel Kaliyo ta tabbatar da kujerar majalisar dokokin tarayya ta ?aramar Hukumar Lere ta jihar Kaduna ga za?a??en ?an Majalisa na jam’iyyar APC Suleiman Aliyu Lere.
Al?alin ya bayyana cewa bayan dogon nazari da binciken Kotun, ya tabbata cewar ?an takarar jam’iyyar PDP da ke kan Kujerar Honorabul Muhammad Rabi’u ba shine halastaccen ?an Majalisar ba, inda nan take Kotu ta kwace Kujerar ta mi?awa Suleman Lere wanda tun asali shine jama’ar ?aramar Hukumar Lere suka zaba.
Da yake zantawa da manema labarai jim ka?an bayan kammala zaman Kotun, Injiniya Suleiman Lere, wanda ake wa lakabi da suna “Gari Ya Waye” ya godewa Allah, sannan ya yi godiya ga jama’ar ?aramar Hukumar Lere bisa addu’o’i da goyon bayan da suka ba shi, har Allah ya sa ya yi nasara.
Za?a??en ?an Majalisa ya kuma yi al?awarin ?orawa akan ayyukan da ya faru na cigaba a majalisa, domin ?aga darajar ?aramar Hukumar Lere da jama’ar baki ?aya.
Injiniya Suleiman Lere ya yi nasara a zaben ?an Majalisar wakilai mai wakiltar ?aramar Hukumar a zaben da aka yi na shekarar 2019.
Daga bisani wata Kotu a birnin tarayya Abuja ta ?wace Kujerar ta ba ?an takarar PDP Muhammad Rabi’u tsawon shekara guda kenan, kafin yanke hukuncin da Kotun koli ta Kaduna ta yi a ranar Laraba inda ta tabbatar da nasarar shi.
