Kaduna: Dillaliyar ‘Yan Bindiga Ta Shiga Hannu

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta samu nasaran hallaka wasu miyagun ‘yan ta’adda 4 masu garkuwa da mutane.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kaduna DSP Muhammad Jalige ya shaida wa manema labarai cewa an jima ana bibiyar ‘yan ta’addan, an datse su akan hanyar Saminaka zuwa Jos suna tafiya a cikin mota kirar Sharon mai launin shu?i.

Lokacin da ‘yan ta’addan suka lura ‘yan sanda na bin diddiginsu akan hanyar Saminaka zuwa Jos, sai suka bude wa ‘yan sandan wuta, a gurin musayar wuta na tsawon mintuna 30 ‘yan sanda suka samu nasaran aika ‘yan ta’addan lahira.

Bayan ‘yan sanda sun duba motar ‘yan ta’addan, sun samu bindigogi kirar AK47 da harsashin bindiga guda 140, sannan ‘yan sanda sun kama wata matar wacce ta ke sana’ar safaran bindigogi da harsashi zuwa ga ‘yan ta’addan a cikin jihar Kaduna.

Related posts

Leave a Comment