An aike wa hudu daga cikin masu nadin sarki biyar na masarautar Zazzau takardar sammaci domin neman jin ba’asi saboda rashin hallartar taron nadin sabon sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli da ya gudana kwanakin baya.
Wadanda aka aikewa takardar sun ha?a da Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Aminu, Limamin Kona Alhaji Sani Aliyu, Limamin Zazzau Alhaji Dalhat Kasimu da Makama Karami Alhaji Mahmoud Abbas.
Taken takardar tuhumar shine: “rashin halartar taron tattaunawa da ma’aikatar kananan hukumomi ta shirya- tuhuma” mai lambobin shaida MLGCA/36/Vol:Vi/1059 da kwanan wata 30 ga Oktoba 2020 dauke da sa hannun Musa Adamu, babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi.
Cikin takardar tuhumar “zaku iya tunawa ranar Juma’a, 30 ga Oktoban 2020, an gayyace ku taro da mai girma kwamishinan kananan hukumomi ya shirya a ofishin sa amma kuka gaza halarta.
“Saboda haka, an baku awa 48 kuyi bayanin dalilin da yasa baza a dauki mataki akan ku ba.”
Rahotanni daga Masarautar ta Zazzau sun bayyana cewar wasu daga cikin masu zaben sarkin, basu ji dadin yadda al’amura ke gudana a masarautar ba.
