Kaduna: An Tsige Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Giwa

Rahotannin dake shigo mana yanzu daga karamar hukumar giwa dake jihar Kaduna na nuna cewa majalisar karamar Hukumar karkashin jagorancin kakakin majalisar, Hon Abdullahi Ismail sun dakatar da Hon Zubairu Alhassan mataimakin Shugaban karamar hukumar kan laifuka guda uku wanda suka hada cin amanar kujerar sa da kuma bayyana sirrin gwamnati tare da rashin girmama majalisar.

Majalisar ta bayyana Hakan ne bayan zaman ta na mako mako inda ta zanta da manema labarai tare da nuna takardar da kansilolin karamar hukumar guda 7 cikin 11 suka sawa hannu.

Daya daga cikin kansilolin, kuma shugaban masu rinjaye na majalisar Hon Hayatu Mu’azu Dallatu ya kara da cewa sun dakatar da mataimakin Shugaban karamar hukumar ta Giwa Honorabul Zubairu Alhassan na tsawon watanni shida kamin su kammala bincike.

Da muka Nemi jin ta bakin dakataccen mataimakin Shugaban karamar hukumar Honorabul Zubairu Alhassan,ya bayana mana cewar wannan matakin shima ji kawai yayi a gari kuma doka ce zata yi halinta.

Related posts

Leave a Comment