Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta samar da jami’an tsaro na musamman da za su ri?a kula da sufurin jiragen ?asa a wani ?angare na matakan magance hare-haren da ake kai wa jiragen da fasinjoji a ?asar.
?aramin ministan sufuri na ?asar Ademola Adegoroye ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyara tashar jirgin ?asa ta Tom Ikimi a ?aramar hukumar Igueben da ke jihar Edo, wadda ‘yan bindiga suka kai wa hari a ?arshen makon da ya gabata tare da yin garkuwa da fasinjoji.
A wata sanarwa da jami’in hul?a da jama’a na hukumar sufurin ?asar ya fitar, ya ce gwamnatin ?asar za ta ?auki matakan da suka dace domin magance matsalar hare-hare kan tasoshin jiragen ?asa domin tabbatar da kariya ga fasinjoji da kayayyakin aikin hukumar.
Daga cikin matakan da ya ce hukumar za ta ?auka har da ha?a kai tsakanin hukumar da al’umma mazauna yankunan da tasoshin jiragen suke domin samar da tsaro da tasoshin jiragen.
Haka kuma ministan ya yi watsi da fargabar da ake yi na cewa gwamnati za ta rufe zirga-zirgar jiragen ?asa a fa?in ?asar, yana mai cewa gwamnatin tarayya da hukumar sufurin jiragen ?asa ba su da wannan niyya, sanna kuma za a ci-gaba da sufurin.
