Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lami?o ya yi shagu?e dangane da halin da ?asa ke ciki na matsalar tsaro inda ya ce “?an Najeriya idan sun ga dama su bar Buhari ya tabbata a mulki har abada.”
Alhaji Sule Lami?o ya bayyana hakan ne a yayin wata hira ta musamman da ya yi da gidan Rediyon BBC Hausa a birnin tarayya Abuja.
Tsohon gwamnan ya kuma ce “jam’iyyar APC annoba ce a Najeriya, ta kawo masifa marar iyaka, gyaran barnar APC nan gaba aiki ne babba, tun da yake ta kawo gaba tsakanin ?a da uwa, da tsakanin wa da ?ani da tsakanin gari da gari, dangi da dangi, addini da addini da kudu da arewa.”
“Amma duk inda ake son mu bayar da gudunmowa za mu bayar wallahi,” a cewarsa.
Sule Lamido ya ce saboda kaunar Buhari da ?an Najeriya suka so ya yi mulki “an ce mana arna, an ce mana kirista, an ce ba ma son Musulunci, ba ma son arewa, komai an yi, an ma ce mu da ?a?anmu ?arayi ne.
“An ce Buhari waliyyi ne, ma’asumi ne, kaza-kaza duk an yi, an ?ata mu.”
Ya ce “idan dai har yanzu ?an Najeriya ba su dawo rakiyar APC ba to sai su tabbatar da Buhari ya yi ta mulki har abada.”
“Tun da suna ganin ya kyauta, to duk mu taru mu ce Buhari don Allah ya ci gaba da mulki har abada.”
Jigon na babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya yi zargin cewa APC mai mulki ta rusa dukkan ginshi?an da aka gina ?asar a kai don tabbatar da ha?akarta.
A cewarsa, hakan ta sa PDP ta du?ufa don ganin ta kar?e mulki da kuma sake lale da nufin ceto Najeriya.
