Gombe: An Garzaya Kotu Domin Tilasta Pantami Takarar Gwamna

Labarin dake shigo mana daga Jihar Gombe na bayyana cewar wasu mazaunan jihar masu kishi sun shigar da ?ara gaban babbar Kotu kan Minista harkokin sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Pantami, domin tilasta masa ya tsaya takarar gwamna a 2023.

Mutanen daga gundumomi 114 dake fa?in jihar Gombe sun shigar da ?arar ne ranar 21 ga watan Maris, 2022, inda suka yi kira da babbar murya ga ministan da lallai ya amince da bukatunsu ko ya gamu da fushin su.

Da yake jawabi a wurin taron manema labarai, shugaban tawagar masu shigar da ?arar, Muhammad Abdullahi, ya ce Sheikh Pantami ya nuna kyakkyawan jagoranci da taimakom matasa a Gombe da ?asa baki ?aya.

A cewar Muhammad Abdullahi, duk wani yunkuri na jawo hankalin ministan ya fito takarar gwamna ya gagara dalilin garzayawar su Kotu kenan, inda ya ?ara da cewa sun yi amanna cewa Ministan ne ya fi dacewa ya karbi jihar.

“Domin tabbatar da abin da muke nufi da gaske ne yasa zamu yi amfani da doka wajen tilasta wa Farfesa Isa Pantami ya fito takara a fafata da shi a za?en fidda gwani na kowace jam’iyyar da yake so.”

Related posts

Leave a Comment