Arise News ta ruwaito cewa tsohon Gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya shilla kasar waje hutawa bayan ziyarce-ziyarcen da ya kai jaje da neman a zabesa a fadin tarayya.
An nemi Tinubu an rasa a wani taron kaddamar da kwamitocin yakin neman zabensa da akayi a Ikeja, birnin jihar Legas ranar Laraba.
Manyan jiga-jigan da suka halarci taron sun hada da Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, jigogin APC, da mambobin kwamitin zaben shugabannin a jihar Legas.
Asiwaju Bola Tinubu ya fara ganawa da Shugaba Buhari makonnin da suka gabata inda ya sanar masa da niyyar takara a zaben shugaban kasa na 2023.
Daga baya ya ziyarci tsohon shugaban kasa na Soja, Ibrahim Babangida IBB. Hakazalika ya kai ziyarar ta’aziyya jihohin Arewa irinsu Neja, Zamfara, da Katsina inda ya bada gudunmuwan miliyoyin kudade don taimakawa iyalan wadanda aka kashe.
Bayan wadannan ziyarce-ziyarcen, Tinubu ya gudu kasar waje ganin Likitocinsa da hutawa. Yayinda wasu majiyoyi ke cewa Landan ya tafi, wasu sunce basu san ainihin inda yaje ba amma sun tabbatar ya tafi kasar waje ganin Likita.
