Jama’ar Kaduna Za Su Dara Da Salon Mulkin Uba Sani – Dahiru Ahmad Mai Ba Gwamna Shawara A Harkar Labarai

An bayyana cewa jama’ar jihar Kaduna za su yi marhabin da darawa bisa salon mulkin sabon Gwamnan jihar Malam Uba Sani saboda kyakkyawar tanadi da ya yi musu.

Mai ba Gwamnan Shawara kan harkokin yada labarai Alhaji ?ahiru Ahmad ya sanar da hakan a tattaunawar sa da wakilinmu ta wayar tarho.

?ahiru Ahmad ya ?ara da cewar da akwai wasu manyan kudurori da gwamnan ya tsara wanda zai ciyar da jama’ar jihar gaba musamman wadanda suke zaune a yankunan karkara.

Mai bada shawarar ya ce kasancewar Uba Sani wanda ya san jihar Kaduna kuma ya karatance ta sosai, hakan ya sanya shi lalubo bakin zare ta fuskar tattalin arziki da tsaro domin inganta rayuwar jama’ar Jihar.

Alhaji ?ahiru Ahmad ya bukaci jama’ar jihar da su sanya Gwamna Uba Sani cikin addu’o’insu domin samun nasara wurin kai jihar gaba.

Related posts

Leave a Comment