Jagoran juyin juya hali na kasar Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya haramta shigar da duk wata allurar riga-kafin korona da Amurka ko Birtaniyya suka samar.
Shugaban ya ce bai amince da su ba, Iran dai tana zaman tankiya da Amurka da Burtaniya na tsawon shekaru da dama.
Yayin wani jawabinsa ta gidan talbijin, Ayatollah ya yaba da ?o?arin Iran na samar da allurar riga-kafinta, ko da yake, ya ce kasar za ta nemo ?arin allurar daga wasu nagartattun wurare.
Wannan yana zuwa ne dede lokacin ake kokarin shigar da riga kafin a kasashen duniya wanda tuni yayi nisa a wasu kasashe.
Sha’anin rigakafin cutar CORONA wani lamari ne da ya ?auki hankulan jama’ar duniya baki ?aya, manyan kasashen duniya na Turai da Larabawa sun amince da shigowa da allurar cikin kasashen su, sai dai wasu kasashen har yanzu suna nuna tababa akai.
