Ina Mamakin Yadda ‘Yan Najeriya Ba Su Ganin Kokarin Gwamnatinmu – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa game da yadda mutane ba sa fita suna yabawa da ?wazon gwamnatinsa, duk kuwa da ?umbin ayyukan raya ?asa da yake ikirarin cewa tana aiwatarwa.

Shugaban kasar ya yi wannan furucin ne a jihar Imo, lokacin da ya kai wata ziyarar aiki ta kwana guda,a ranar Talata.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya karbi ragamar mulkin Najeriya a wani lokaci da kasar ta samu kanta a tsaka mai wuya.

Adadin man da ?asar take ha?a ya ragu sosai, farashinsa a kasuwannin duniya ya fa?i ?asa warwas amma duk da haka, gwamnatinsa ta san yadda take ?u?utawa take aiwatar da ayyukan raya ?asa da kuma inganta tsaro a Najeriya.

Shugaban ya ?ara da cewa idan wani na kokwanto, to ya tambayi al’ummar jihar Borno don jin yadda aka karya lagon ?an Boko Haram!

Sai dai wani abin takaici, a cewar Shugaba Buharin shi ne yadda mutane ke kau da kai – ba sa yabawa – kamar yadda ?an magana ke cewa abin kirki bai gaji kare ba – wato ko ya yi ma jifar sa ake yi.

“Daidai wa daida, idan aka yi la’akari da lokaci da ?an abin da ake samu, wannan gwamnatin ta yi rawar-gani ?warai da gaske.

“Dole ne na fa?a, saboda wa?anda ya kamata su fa?a ba sa fa?a, kuma ban san dalili ba,” in ji Shugaba Buharin.

Related posts

Leave a Comment