Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai na ci gaba da shan caccaka daga bakin ?an Najeriya, bayan da ya bayyana cewa Jihar Kaduna ta ri?a kashe wa kowane mai cutar Korona naira 400,000 kafin ya warke.
El-Rufai ya yi wanann bayanin ne a taron Majalisar Sarakunan Arewa, da ya gudana a Kaduna, kuma ya watsa bayanin na sa a shafin Twitter.
A wurin taron ya ?ara tabbatar da cewa sai fa a ci gaba da hattara, domin har yanzu cutar Korona na nan, ba a rabu da ita ba.
Ya ce cuta ce mai cin ku?ade, domin Jihar sa Kaduna ta ri?a kashe naira 400,000 a kan duk mai cutar Korona mutum daya kafin ya warke.
Wannan bayani bai yi wa ?an Najeriya da?i ba, inda nan da nan su ka bi shi a guje har cikin shafin sa na Twitter su na caccaka da ragargazar sa.
Idan ba a manta ba, kwanan baya Kwamishinan Harkokin Lafiya na Jihar Lagos, ya bayyana cewa Lagos ta ri?a kashe har naira milyan 1 a kan Mai cutar Korona da ya kusa kai gargarar mutuwa. Shi ma ?in dai ya sha caccaka kamar El-Rufai.
Dukkan su biyu ?in dai sun ?an?ana ciwon Korona sun san zafin sa.
