Ministar kudi, Zainab Ahmad, ta ce matsala ta farko da ke damunta ita ce ‘haraji’, ta biyu ‘haraji’, haka ma ta uku ita ce ‘haraji’ matsalar zirarewar haraji ta na hanani bacci da ido biyu a bude.
Zainab ta bayyana hakan ne yayin da ta ke amsa tambayoyi a wurin wani taro da aka yi domin murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yanci.
Zainab Ahmad ta amsa tambayar da Poju Oyemade, babban Fasto a cibiyar al?awarin kirista (covenant christian church) yayin gudanar da wata tattaunawa da aka shirya domin murnar zagayowar ranar samun ?anchin-?asa.
A yayin da aka tambayeta abubuwa uku da suke hanata bacci sai ministar tace; ”Abu na farko shine haraji, na biyu ma haraji, hakama na uku haraji.”
Sai dai, Ministar ta ce ma’aikatar ta na aiki tu?uru don ganin ta ya?i ?aranchi da zirarewar haraji, wanda hakan ke hana samun isassun ku?in-shiga ga ?asa.
Ta cigaba da cewa; ”ma’aikatata ta fara amfani da hanyoyin fasahar zamani don ganin an samu daidaito a tsarin karba da tattara haraji na ?asa. “Mu na yun?urin hana zirarewa da kuma inganta ha?inkan mutanenmu, musamman dangane da tsarin karba da tattara haraji.
Mun kawo sa hannun jari a tsarin sadarwa na zamani, sannan kuma mu na yun?urin ganin tattara abubuwa wuri guda.
”Muna da tsarin zama duk wata mu bibiyi tsarin harajinmu sannan mu tattara al?aluma. Mu na aiki domin ?ara sanin duk wasu hanyoyin zamani da za su ba mu ikon ganin biyan harajin kamfanoni akai-akai ko in lokaci ya kusa.”
Ministar ta ce Nijeriya ta samu gagarumar nasara da kuma cigaba ta ?angaren wadata kanta da abinci. “Munayin duk iyakacin ?o?arinmu don mu tabbatar ?asarmu ta wadatu kwarai, musamman a ?angaren kayan masarufi da sauran kayan abinci”
Sannan ta kara da cewa; “dole na sanar da cewa mun samu gagarumar nasara a wannan ?angaren, saboda ba don mun wadatu da abinci ba a lokacin kulle, da babu shiga, ba fita a ?asa, da mun fa?a cikin gagarumar matsala”.
