Rahotanni daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya na bayyana cewa Shugaban Hukumar Ya?i da Almundahana a Ma’aikatun Gwamnati (ICPC), Bolaji Owasanoye ya bayyana cewa ICPC ta bi diddigin kasafin ku?i na 2021, inda ta gano akwai wuru-wurun maimanta sunayen ayyuka sau biyu har ayyuka 257 a cikin Kasafin Ku?a?e na 2021.
Bolaji ya ce ICPC ta gano wannan mummunar har?alla ce bayan ta yi wa kasafin filla-filla.
Ya ce adadin ku?a?en da aka dafkara a cikin kasafin za su kai naira biliyan 20.138.
Bolaji ya zargi ma’aikatun da ministoci daban-daban ke jagoranta da kuma sauran hukumomin gwamnati da satar ma?udan ku?a?e ta hanyar cushe a cikin kasafin ku?i, dan?ara sunayen ma’aikatan bogi da kuma sauran laifukan zamba.
