Kungiyar Taliban ta fitar sabuwar doka da ta yi kira a ?auki matakin da ya dace don tabbatar da ‘yancin mata a Afganistan.
Umurnin dokar ya ce kada a tilasta wa mata aure, sannan kuma ta yi bayani kan ha??in mallakar dukiya idan mijin mace ya mutu.
Amma babu maganar ha??in aiki ga mata ko kuma batun da ya shafi ilimi.
Ha??in mata ya zama abin damuwa tun lokacin da Taliban ta kar?i ikon Afghanistan a watan Agusta
Kusan an umarci mata su kasance a gida ba zuwa makaranta, kuma a watan da ya gabata an haramta wa mata fitowa a shirye shiryen talabijin.
