Hedkwatar tsaron Najeriya ta umarci manyan sojoji da suka haura kwas na 39 a makarantar horas da manyan sojoji da su ajiye aiki bisa ra?in kansu.
Matakin na zuwa ne bayan da Bola Ahmed Tinubu ya na?a sabbin hafsoshin tsaron ?asar.
Hakan na ?unshe ne cikin wata sanarwar mai ?auke da sa hannun Manjo janar Y. Yahaya a madadin babban hafsan tsaron ?asar.
“An umarce ni na bu?aci duka manyan sojoji da ke sama da kwas na 39 na makarantar horas da manyan hafsoshin sojin ?asar, su gaggauta mi?a takardun ajiye aiki bisa ra?in kai”, in ji sanarwar.
“Haka kuma ana bu?atar wa?anda umarnin ya shafa su mika takardun nasu ga shalkwatocin tsaron da suke aiki zuwa ranar Litinin 3 ga watan Yulin 2023”.
