Gidauniyar Aliko Dangote ta bayar da tallafi ga wasu ‘yan Najeriya da ya?in Sudan ya tilasta musu komawa ?asar.
Mutane 125 da suka koma Najeriya ranar Asabar da ta gabata suka ha?ar da gajiyayyu, kowannensu ya samu tallafin naira 100,000 da wasu kayyakin ihsani a cikin jaka, daga gidauniyar ta Dangote.
A cikin watan Mayu fiye da mutum 2,278 suka samu tallafin 100,000 kowannensu da abubuwan ihsani domin samun saukin ha?uwa da iyalansu, bayan dawo da su ?asar daga Sudan.
Daga cikin mutanen da aka kwaso cikin makon da ya gabata har da wasu tsofaffi biyu da suka yi shirin zuwa Umara a mota, hanya ta bi da su ta birnin Khartoum, suka kuma fa?a tarkon ya?in da ake gwambazawa a birnin, lamarin da ya sa suka rasa duka guzurinsu.
Wani dattijo mai suna Muhammad Saidu Ahmed ya ce ”Na dawo daga Sudan ba tare da ko sisi ba, amma yanzu na samu 100,000”.
