Hatsarin Mota Ya Lakume Rayukan ‘Yan Bautar Kasa Biyar


Mummunan hadarin da ya afku jiya Laraba a babbar hanyar Abaji zuwa Kwali dake Babban birnin tarayya Abuja, ya yi sanadiyar mutuwar alkalla Matasa masu yi wa kasa hidima guda biyar.

Babbar Daraktar yada labarai da Hulda da jama’a na hukumar ta NYSC, Adenike Adeyemi ta fitar da wata sanarwa Mai taken “Ranar Laraba Mai Muni ga iyalan hukumar NYSC” wato ” Black Wednesday for NYSC Family” a turan ce.

Ta ce, “Cikin jimami da bakin ciki Darakta Janar, da daukacin hukumar NYSC ke jajanta wa, iyalan matasan dake shirin fara bautan kasa, da suka rasa rayukansu a hadarin motan da ya auku, misalan karfe 2 na daren jiya, Laraba, 28 ga Yulin Shekarar 2020, a babban titin Abaji dake Kwali.” Inji sanarwar.

“Hakazalika Dirakta Janar da daukacin hukumar na jajantawa gwamnatin jihar Akwa Ibom da na Imo, kan wannan hadarin da ya yi sanadiyar rasuwar matasan masuyiwa kasa hidima.”

Related posts

Leave a Comment