Daukewar Facebook Da WhatsApp: Mamallakin Kamfanin Ya Nemi Gafarar Duniya

Wanda ya ?ir?iro Facebook, Mark Zuckerberg, ya nemi gafara ga biliyoyin mutane a fadin duniya sakamakon katsewar shafukansa.WhatsApp, da Instagram da shi kansa Facebook sun daina aiki na awanni shida amma a yanzu sun dawo.

Lamarin ya hana mutane biliyan uku da rabi da ke amfani da shafukan damar shiga.

Masu sharhi na hasashen cewa matsalar da aka samu a jiya, na iya janyo wa kamfanin asarar da ta kai ta sama da dala miliyan 3, na harajin talluka a iya wannan taki.

Lamarin na faruwa ne kwana guda bayan wata mai bankada da ta taba aiki da kamfanin ta fallasa cewa Facebook ya fi fifita ribar da yake hankoron samu fiye da kare masu amfani da shafukansa.

Related posts

Leave a Comment