Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kwamitin rikon kwarya na jam’iyya mai mulki APC ya ce har yanzun gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ne shugaban ri?on jam’iyyar.
Da yake jawabi ga manema labarai a Sakatariyar APC ta ?asa dake Abuja, Kakakin Kwamitin rikon jam’iyyar Ismaeel Ahmed, ya ce ya gaza gane meyasa lamarin ke ru?a wasu mutane bayan babu wani dalili na cire Mai Mala Buni daga shugabancin.
“Wani ya tambaye ne menene makomar Mala Buni a jam’iyya, inaga wannan abu ne mai sauki, ban san meyasa mutane da yawa suka gaza fahimta ba.” “Tun da aka kafa kwamitin rikon kwarya ranar 25 ga watan Yuni, 2020, duk lokacin da shugaba baya nan, gwamna Bello ke wakiltarsa.
“Muna da babban taro ranar 26 ga watan Fabrairu, Buni ya rubuta wasikar damka mulki a hannun Bello domin ya tafi duba lafiya.
Abu ne na gaggawa da ya shafi lafiya. Mu kuma muna da babban taro, ba zamu jira har sai ya samu lafiya ba.”
Ahmed ya ?ara da cewa kasancewar shugaba baya nan, gwamna Bello ya karbi cikakken ragamar tafiyar da APC kuma nauyin komai ya koma kansa. “Abu ne mai sauki kuma a bayyane, idan akwai wanda lamarin bai masa da?i ba, yana da damar zuwa Kotu.
