Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar sanannen dan kasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata, ya ce salon mulkin da ake tafiyar da Najeriya ya gaza, ta fuskoki da dama.
Dantata ya furta hakan ne yayin da ya karba bakuncin kungiyar dattawan arewa wadanda su ka je mishi ta’aziyyar Sani Dangote, Bashir Tofa da sauran manyan mutanen jihar Kano da su ka rasu babu dadewa.
Ya ce akwai bukatar dattawan arewa su hada kai tare da sauran ‘yan Najeriya wurin kawo wata mafita da za ta kawo karshen matsalolin Najeriya.
“Za ku yarda idan nace yanayin salon da ake bi wurin mulkin Najeriya ya gaza don haka ya kamata su sauya wani salon na daban,” a cewarsa.
Wadanda suka je ta’aziyyar sun hada da Janar Sale Maina, Hakeem Baba Ahmed, shugaban kungiyar hadin kan arewa, Nastura Shariff, Dr Sadiq Gombe, Hajiya Najaatu Mohammed da sauransu.
