Hanci Da Rashawa: Najeriya Na Asarar Triliyan Biyu Da Rabi Duk Shekara – Masana

An bayyana cewar Najeriya na yin asarar kwata na kasafin kudinta da yakai kimanin Naira Triliyan Biyu da rabi duk shekara ta sanadiyyar cin hanci da rashawa.

?ungiyar ?ididdiga da kariya daga zamba ta ?asa (SFAFP) ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar.
?ungiyar ta bayyana cewar ana samun faruwar hakan ne ta hanyar amfani da kayayyaki gwamnati ta haramtacciyar hanya da ?in biyan haraji da kayayyakin da ake shigowa da su.

?ungiyar ta cigaba da cewar sauran hanyoyin sun hada da zamba gami da ?wange da biyan albashi ga ma’aikatan bogi bayar da cin hanci gami da aringizo da sauran bada?aloli masu yawa.

Shugaban kungiyar Iliyasu Gashinbaki yace kungiyar zata taimaka wajen fallasawa da bankado dukkanin wata bada?ala da ake amfani dasu wajen ha’intar gwamnati.

Gashinbaki ya kara da cewar cuwa cuwar ba wai kawai a Najeriya ake samun ta ba, ta ha?a da sauran ?asashen nahiyar Afirka.

Ya bayyana cewar a wani bincike da aka gudanar a kwanan nan ya nuna cewa mafiyawan kasashen Afirka na fuskantar matsalolin ta?arbarewar arziki da tarin basussuka ne biyo bayan yadda cin hanci da rashawa rashawa ke illa ga ‘yan ku?a?en da suke samu.

Related posts

Leave a Comment