2023: Ban Damu Da Wanda Zai Zama Shugaban Kasa Ba – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, ya ce shi bai damu da wanda zai gaje shi ba a matsayin shugaba a shekarar 2023.

Buhari ya tabbatar da hakan ne a hirarsa da gidan talabijin na Channels TV a birnin tarayya Abuja.

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa “Za?en 2023 ba matsalata ba ce”.

“Ban damu da wanda zai gaje ni ba, rabu da shi ya zo ko ma wane ne,” in ji shi.

Da ya ke amsa tambaya kan ko me ke zuwa masa a rai idan ya ji an ambaci za?en 2023, Buhari ya amsa da cewa: “Ba matsalata ba ce.

Na tabbata na ajiye rahoton duk wani abu mai muhimmanci, bai kamata wani ya kira ni ba da shaida a gaban kotu ba.

Related posts

Leave a Comment