Hukumar Alhazai ta ?asa (NAHCON) ta bayyana cewa insha Allahu jirgin farko da zai kwashi kashin farko na mahajjatan bana zai bar Najeriya zuwa Saudiyya mako mai zuwa, hukumar ta sanar da cewa za’a fara jigilar mahajjatan bana 2022 daga Najeriya a ranar 9 ga watan Yuni, 2022.
Da yake jawabi yayin sanya hannu kan yarjejeniya da kamfanonin da zasu yi aikin a Abuja ranar Jumu’a, shugaban NAHCON, Zikirullah Hassan, ya ce sun za?i ranar ne domin kammala duk wasu shirye-shirye.
Ya kuma bayyana cewa sun za?i kamfanonin jiragen sama uku da zasu yi aikin jigilar Alhazan kuma sune; Azman Air, Max Air da kuma Flynas Airlines.
Ya roki kamfanonin jiragen uku da su yi aiki mai kyau ba tare da yin karan tsaye ga dokokin ma’aikatar sufurin jiragen sama ba kuma su mu’amalanci mahajja da kyau.
Hassan ya kuma bayyana cewa a ranar 6 ga watan Yuni, tawagar hukumar NAHCON zasu nufi Makkah da Madina domin ?arasa shirye-shirye a can.
“Yau ta kasance rana mai dumbin tarihi saboda rana ce ta farko a ayyukan aikin hajjin bana 2022. Mun sani cewa idan babu jiragen sama mutanen da ke wajen Saudiyya ba zasu samu damar sauke farali ba.”
“Ku bani dama na taya kamfanonin jirgen da suka yi nasara murna, da su muke fa?i tashi a hukumar nan tun tale-tale. Haka nan muna fatan wa?anda ba’a za?a ba zasu yunkuro nan gaba.”
