2023: Takarar Atiku Ta Firgita APC – Waziri

Wani jigo a cikin dattawan babbar jam’iyyar hammayya ta PDP Alhaji Adamu Maina Waziri ya ce jam’iyyar APC mai mulki ta tsorata da dan takarar da suka fitar shi ya sa take kwan-gaba-kwan-baya wajen fitar da dan takararta na zaben 2023.

A hirarsa da BBC Alhaji Maina Waziri ya yi zargin cewa tun da farko ma APC ce ta yi manakisa har hukumar zaben kasar t kara wa’adin sati daya na zaben fitar da dan takara bayan su sun riga sun shirya gudanar da zabensu a lokacin.

Tuni dai babbar jam`iyyar hamayyar ta PDP ta yi nata zaben, inda tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar ya yi nasarar samun takarar shugaban kasar. Jigon ya ce abin da PDP ta yi na fitar da dan takararta ya ba wa abokan hamayyar tasu mamaki, yadda suka hada kai su ka yi wannan zabe.

Kuma wannan nasara da Atikun ya samu, kamar yadda masana siyasa ke cewa ka iya wargaza lissafin jam`iyyar APC, lamarin d masanan ke ganin alamunsa yadda ake ta kai ruwa rana a yanzu kan yadda jam’iyyar za ta kai ga fitar da dan takarar.

Wannan ya sa hankali ya koma kan  jam`iyyar APC mai mulki don ganin yadda zaben fitar da gwani na masu neman takarar shugaban kasa zai kaya. A ranar  Litinin mai zuwa ne ake sa ran gudanar da zaben fitar da gwanin.

Dattijon na PDP ya ce, yanzu APC ta shiga tsaka mai wuya kan yadda ta bullowa lamarin fitar da dan takarar da zai kara da nasu a babban zaben, inda yake cewa, ” Duk wanda yake kasar nan ya san cewa ana kwan-gaba-kwan-baya, yaya za su yi su fitar dan takara ba za su iya yi ba, wallahi muna jiransu, wallahi ina gaya maka mu ba ma yanzu fargaba, mutanen nan sun nuna ragwanci don sun firgita mun yi abin da ba su taba tsammani ba.”

Ya kara da cewa, fatansu yanzu shi ne ita kanta APC ta samu nasarar fitar da dan takararta lami lafiya, ” yanzu su muke jira kuma muna addu’a su yi taronsu lafiya, don rashin zamansu lafiya zai iya kawo rashin zaman lafiya a kasar nan,” in ji shi.

Alhaji Maina Waziri ya ce, kishin arewacin kasar da kuma burin kare martabarta ne ya sa a lokacin zaben fitar da gwaninsu, ya sa gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Tambuwal ya janye tare da mara wa Atiku baya ya yi nasara.

Ya ce sun lura cewa wani daga daya bngaren kasar na kudu ya yunkuro zai yi amfani da kudi a zaben ya yi nasara wanda hakan ba karamar illa zai yi ga arewacin Najeriya ba.

Saboda haka ne Aminu Tambuwal ya nuna kishi da jaruntaka ya janye a wannan takara domin hada kai da Atiku Abubakar, wanda hakan ba karamin alfanu ba ne ga yankin arewacin Najeriya.

Related posts

Leave a Comment