Hukumar lafiya ta Saudiyya ta ce akalla mahajjata bakwai ne suka mutu sakamakon tsananin zafin rana da ake fuskanta a ?asar, wanda ya haura maki 40 a ma’aunin salshiyos.
Mai magana da yawun ma’aikatar ya ce a ranar Laraba ka?ai an samu mutum 2200 da zafin ranar ya yi musu illa, ciki har da fiye da mutum 250 da zafin ya kayar da su.
Rahotanni dai sun bayyana cewar hajjin Bana ya samu karbuwar Mahajjata masu yawa wanda ba a samu ba a tarihi a baya, inda aka ?iyasta cewa kimanin alhazzai miliyan biyu da rabi ne daga sassan duniya daban daban suka yi hawan arfa a bana.
