Hajjin Bana: Akwai Babban Kalubale Ga Alhazzan Najeriya A Bana – Majalisar Koli Ta Addinin Musulunci

IMG 20240310 WA0411

Majalisar Koli ta addinin Musulunci a Najeriya ta bayyana damuwa a game da babbar barazanar da ke tattare da aikin Hajjin bana ga al’ummar Musulmi a Najeriya.

Binciken da majalisar ta gudanar kan shirye-shiryen aikin Hajjin na bana ya nuna akwai wagegen gi?i a game da shirye-shiryen.

Wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta ce wa’adin da hukumomin Saudiyya suka ?iba game da kammala duk wani shiri da ya kamata kama daga biyan ku?in kujera zuwa sauran shirye shirye, akwai yiwuwar zai iya cika ba tare da maniyyatan bana sun san halin da suke ciki ba na ainihin ku?in da ya kamata su cika kan kujerar.

Majalisar ta ce har kawo yanzu ba a biya ku?in rabin kujerun da aka ba wa Najeriya ba.

“Babban abin damuwar shi ne mutanen da suka fara biyan wani daga cikin ku?in kujerar aikin Hajjin na bana, har yanzu suna cikin rashin sanin inda suka dosa,” in ji sanarwar.

Daga bisani majalisar ta ce tana sane da irin ?o?arin da gwamnati ke yi wajen samun sauki musamman kan batun canjin dala wanda shi ne musabbabin abin da ya janyo wannan matsala.

Ta kuma bu?aci ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da kuma masu ruwa da tsaki da su taimaka yadda ya kamata domin ganin ba a samu koma baya a aikin Hajjin bana ba ga maniyyatan Najeriya.

Related posts

Leave a Comment