Gyaran Dokar Za?e: INEC Ta Bu?aci ‘Yan Majalisa Da Aiki Ba Tare Nuna Bambanci Ba

Shugaban Hukumar Za?e ta ?asa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi kira ga ‘yan Majalisar Tarayya da su yi aiki ba tare da la’akari da jam’iyyar da kowanne ke wakilta ba wajen yi wa Dokar Za?e garambawul wanda zai taimaka wajen inganta yadda ake gudanar da za?e a ?asar nan.

Yakubu ya yi wannan kiran ne a wajen bikin ?addamar da kwamitin ha?in gwiwar ?wararru na yi wa Dokar Za?e kwaskwarima wanda aka yi a Abuja a ranar Juma’a.

Kwamitin Ha?in Gwiwar Majalisar Tarayya kan Hukumar Za?e da Al’amuran Za?e ne ya shirya taron tare da tallafin Cibiyar Tsare-tsare da Aikin Doka, wato Policy and Legal Advocacy Centre (PLAC) da kuma Ofishin Harkokin ?asar Wajen Birtaniya da Cigaban Kwamanwal, wato UK Foreign and Commonwealth Development Office (FCDO).

Mista Festus Okoye, wato Babban Kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin ya?a labarai da Wayar da kan masu za?e a hukumar, shi ne ya wakilci Mahmood a taron.

Yakubu ya ce garambawul ?in ya zo a kan kari, kuma abu mafi muhimmanci shi ne lallai a tabbatar da cewa gyare-gyaren sun yi tasiri, kuma an yi su ba tare da kallon kowace jam’iyya ba, sannan a cire duk wata rarrabuwar kai, kuma a kammala su a?alla daga yanzu zuwa watanni hu?u na farko na shekarar 2021.

Idan an tuna, tun a cikin 2020 ne shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya yi al?awarin cewa Majalisar Tarayya za ta bada ha?in kai wajen zartar da gyaran Dokar Za?e ya zuwa ?arshen watanni hu?u na farko na shekarar 2021.

Shugaban na INEC ya yi na’am da sabon yun?urin da kuma sadaukarwar da shugabannin Majalisar Tarayya su ka nuna wajen yi wa tsarin dokokin gudanar da za?e kwaskwarima.

Yakubu ya ce sabon ho??asan da majalisar ke yi ya zo a kan kari kuma tilas ne a ci gaba da shi tare da aiwatar da shi a cikin tunanin waiwaye da kuma hanzari.

Ya ce lallai ne a tabbatar da yun?urin ya tafi bisa hanyar kammaluwar sa, hanzari, saka hannu da tunanin dabaru.

Yakubu ya ce hukumar ta sadaukar da kai sosai ga tabbatuwar aikin garambawul ?in kuma za ta ci gaba da bada shawarwari da za su taimaka wajen ingantuwar harkokin za?e a ?asar nan.

Ya ?ara da cewa gyara tsarin dokokin za?e ba wai zai haifar da sauyi farat ?aya wajen aikin gudanar da aikin za?e ba.

Ya ce: “Tsarin Mulki da kuma Dokar Za?e ba su iya yin aiki da kan su, kuma dukkan su su na motsawa ne ta hanyar ayyuka ko rashin ayyukan masu ruwa da tsaki a tsarin za?e.”

Wani memba a kwamitin ?wararrun, Malam Sadiq Mu’azu, ya yi nuni da cewa ?aya daga cikin alfanun yi wa Dokar Za?e gyaran fuska shi ne zai tattaro dukkan gyare-gyaren a cikin kundi guda ?aya.

Mu’azu ya ce babban burin garambawul ?in shi ne domin a tabbatar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa sun kula da ha??in maza da mata tare da kawar da duk wani nau’i na bambanci daga cikin jam’iyyun siyasa.

Ya ce, “Dokar ta bu?aci dukkan jam’iyyun siyasa da su tabbatar da cewa shugabanni mata su ne mata ba maza ba kuma dukkan shugabannin matasa za su kasance ‘yan shekara tsakanin 18 zuwa 45 daga ranar da aka yi za?u??ukan wa?annan mu?aman.

“Kuma dokar ta na so a ?ara yawan ku?in da ‘yan takarar zama Shugaban ?asa ko Gwamna ko Sanata ko ?an Majalisar Tarayya za su iya kashewa a kamfen.

Ya ce: “An ?ara ku?in da ?an takarar Shugaban ?asa zai iya kashewa daga naira biliyan ?aya zuwa naira biliyan 5, sannan an ?ara na ?an takarar gwamna daga naira miliyan 200 zuwa naira biliyan 1, sai kuma aka ?ara na ?an takarar Sanata zuwa miliyan 100, na ?an Majalisar Wakilai kuma zuwa miliyan 70.”

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Hukumar Za?e a Majalisar Dattawa, Sanata Kabiru Gaya, ya ce idan an zartar da dokar kuma aka amince da ita, to za ta taimaka gaya wajen sauya fasalin siyasar ?asar nan.

Ya ce: “Ba shakka, yi wa Dokar Za?e garambawul zai yi tasiri mai kyau matu?a a kan hanyoyin gudanar da za?e wa?anda sun sha gamuwa da ?alubale a baya tare da tada muhawarori wa?anda su ka yi barazana ga bu?atar yin za?e cikin ‘yanci, adalci da inganci.”

Ya ce an ?addamar da Kwamitin ?wararru ?in ne domin a cimma iyakance lokacin da za a amince da dokar ya zuwa ?arshen kwatar farko ta shekarar 2021.

Shi kuwa Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, al?awari ya yi na yin aiki tare da kwamitin ?wararrun domin tabbatar da ba a samu cikas ba wajen samun amincewar shugaban ?asa ga dokar.

Malami, wanda mai taimaka wa shugaban ?asa ta musamman kan gyaran fuskar harkokin shari’a da hul?a da ?asar waje, Misis Juliet Ibekaku-Nwagwu ta wakilta, ya ce, “Zan ci gaba da aiki kafa?a da kafa?a da Majalisar Tarayya don tabbatar da a ?arshe kwaskwarimar ta samu amincewa kamar yadda aka tsara.

“Na tuna da cewa ba a da?e da gama za?u??ukan 2015 ba, Shugaban ?asa ya amince da ?addamar da kwamitocin gyaran fuskar tsarin mulki da dokokin za?e a cikin 2016, kuma mu na ta aiki tare da Majalisar Tarayya kuma mun fito da dokoki hu?u wa?anda Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta yarda da su kuma ta aika da su zuwa Majalisar Dokoki.”

A sa?on sa na sa alheri, ahugaban sashen gudanar da mulki na FCDO, Mista Sam Waldock, ya ce ?asar Birtaniya ta na alfahari da goyon bayan da ta ke ba tsarin mulkin dimokira?iyya na Nijeriya.

Ya ce, “A cikin shekaru biyar da su ka gabata, Birtaniya ta kashe sama da fam miliyan 50 a kan tsarin dimokira?iyyar Nijeriya kuma ita ce ?asa mafi girma a Afrika mai bin tafarkin mulkin dimokira?iyya kuma ta na cikin manyan membobin Kwamanwal.

“Mu na jinjina wa Majalisar Tarayya a kan aikin ta na yi wa wannan doka garambawul wanda zai taimaka sosai har ma bayan an yi za?e.

“Kafa kwamitin ?wararru da aka yi don a hanzarta aiki a kan wannan doka ya na da matu?ar muhimmanci wajen bada gudunmawa ga tsarin dokokin za?e na Nijeriya.”

Shi ma a jawabin sa, Babban Daraktan PLAC, Mista Clement Nwankwo, ya bayyana jin da?i kan ganin za a zartar da dokar a cikin ?an?anen lokaci.

Ya ce, “Sakamakon ganin yadda aka kasa a yun?urin baya na rattaba hannu kan Dokar Za?en a cikin 2018, a bayyane ya ke cewar wannan sadaukarwar ta samu amincewar kowa da kowa daga kowane ?angare, wanda hakan ya nuna kenan yanzu mun samu sabuwar Dokar Za?e.

”Tare da goyon bayan Ofishin Harkokin ?asar Wajen Birtaniya da Cigaban Kwamanwal, mun samu nasarar yin ha?in gwiwa da Majalisar Tarayya don ganin an cimma burin da majalisar ta ke so a cimmawa.”

Related posts

Leave a Comment