Gwarzon Kare ‘Yancin Bakar Fata Desmond Tutu Ya Mutu

Fitaccen ?an gwagwarmayar nan ta ?wato ?ancin ba?a?e a Afirka ta Kudu, Acibishof Desmond Tutu ya rasu.

Fadar Shugaban ?asar Afirka ta Kudu ce ta sanar da rasuwar Tutu, wanda ya lashe kyautar gwarzon zaman lafiya ta duniya.

Fadar ta ce Acibishof Tutu ya rasu a yau Lahadi ya na da shekaru 90 da haihuwa.

Kawo yanzu dai fadar shugaban kasar ba ta baiyana abin da ya haifar da rasuwar ta sa ba.

Sai dai kuma tun a shekarar 1990 likitoci su ka gano ya kamu da cutar jeji, inda ya sha fama da jigilar asibiti a kan ciwon.

A shekarar 1984 ne dai a ka baiwa Tutu kyautar gwarzon zaman lafiya sakamakon gwagwarmayar ya?i da kin jinin bakake ba tare da wata rigima ba.

Related posts

Leave a Comment