Gwamnoni Ne Suka Jefa ‘Yan Najeriya Cikin Talauci – Fadar Shugaban Kasa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ?ar?ashin jagorancin shugaban ?asa Muhammadu Buhari ta dora alhakin katutun talaucin da ke damun Najeriya kan gwamnonin jihohi.

Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare, Clem Agba ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya ranar Laraba, kamar yadda gidan talbijin na Channels TV ya rawaito.

Ya ce shirin gwamnatin tarayya na kyautata rayuwar ‘yan kasar bai yi tasirin da ya kamata ba ne saboda gwamnonin jihohi ba su bai wa gwamnatin tarayya hadin kai ba.

Mr Agba ya kara da cewa gwamnonin sun fi mayar da hankali wajen aiwatar da ayyukan da ba su da muhimmanci, maimakon inganta rayuwar al’ummar karkara.

A wani labarin na daban Gwamnonin Najeriya 36 sun sake maka Gwamnantin Shugaba Muhammadu Buhari ?ara a Kotun ?oli, inda su ke neman kotu ta tilasta wa Gwamnatin Tarayya ta maida masu ku?a?en harajin naira biliyan 176 da Gwamnatin Tarayya ta kar?a a hannun mutane a fa?in jihohin ?asar nan.

Ma?udan ku?a?en da ake tankiya a kan su ?in dai Gwamnatin Tarayya ta kar?e su ne tsakanin 2015 zuwa 2020 a jihohin Najeriya, da sunan ‘Harajin Stamp Duties’.

Harajin ‘Stamp Duties’ dai wasu ku?a?e ne da Gwamnatin Tarayya ke tatsa a jikin kowane ?an Najeriya, a duk jihar da ya ke idan ya ciri ku?i a asusun sa na banki, ko kuma ya tura ku?i a wani asusu daga asusun ta, ko ta waya, ko ta POS ko ta na’urar ATM ko kuma kai-tsaye daga cikin banki.

Wa?annan ku?a?en ne jihohin Najeriya su ka ce kowace jiha ke da ha??in kar?ar su a jihar ta, ba ha??in gwamnatin tarayya ba ne kar?ar ku?a?en.

Bisa wannan dalili ne kowane Antoni Janar na jihohi 36 ya shigar da ?ara a madadin jihar sa a Kotun ?oli. Kuma kowace jiha ta ?auki lauyan ta, inda su ke neman Gwamnatin Tarayya ta maido masu jimlar Naira biliyan 176 da ta tatsa a cikin jihohin ?asar nan daga 2015 har zuwa ?arshen 2021.

Wannan dambarwa ta taso a daidai lokacin da Babbar Kotun Tarayya ta Fatakwal ta haramta wa Gwamnatin Tarayya kar?ar Harajin VAT a Jihar Ribas, inda kotun ta ce harajin VAT ha??in gwamnatin jiha ne, ba na gwamnatin tarayya ba ne.

Tuni ita ma jihar Legas har Majalisar Dokokin ta sun kafa dokar daina biyan VAT ga Gwamnatin Tarayya a Jihar Legas, sai dai a ri?a biya ga gwamnatin jiha.

Haka kuma wanann dambarwa ta zo ne wata ?aya bayan Gwamnatocin Jihohi 36 sun kafsa jayayya da Gwamnatin Tarayya kan batun biyan wasu ‘yan gidoga Naira biliyan 171 daga asusun jihohi da ?ananan hukumomi.

Related posts

Leave a Comment