Gwamnatin Tarayya Za Ta Ba Ilimi Fifiko Domin Samar Da Kyakkyawar Al’umma

Rahotanni daga birnin Daura ta Jihar Katsina na bayyana cewar Shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa inganta ilimi a ?asar nan zai cigaba da kasancewa a sahun gaba wajen abubuwan da gwamnati zata fi baiwa muhimmanci domin samar da kyakkyawar al’umma nan gaba.

Shugaban ya fa?i haka ne yayin da ya kar?i bakuncin ?alibai da shugaban makarantar Premier Pacesetters a gidansa dake Daura, jihar Katsina ranar Alhamis a ziyarar barka da Sallah da suka kai mishi.

“Shugaba Buhari ya ?ara tabbatar da za’a ?ara himma sosai domin samar da cigaba a ?angaren ilimi.” “Zamu ?ara yawan ku?a?e a ?angaren ilimi don samar da cigaba a koyo da koyarwa a kokarin mu na farfado da ?angaren ilimi a Najeriya.”

Shugaban Kasa Buhari, wanda ya ?auki lokaci tare da ?alibai ?ananan yara, ya jaddada muhimmancin ?abi’a mai kyau a wajen neman ilimi, ya kuma ro?e su kada su gaza a karatunsu.”

“Malamar makarantar, Mrs. Celine Friday, ta isar da sakon barka da sallah ga shugaban a madadin malamai da ?aliban makarantar baki ?aya kuma ta yaba wa gwamnatinsa bisa kulawa ta musamman da take baiwa ilimi.

Ta kuma yi amfani da wannan damar wajen mika kokon bara ga gwamnatin tarayya da ta taimakawa makarantu masu zaman kansu musamman na yankunan karkara.”

Related posts

Leave a Comment