Gwamnatin Tarayya Ta Rage Harajin Shigowa Da Kayayyaki

Shugaban hukumar yaki da masu fasa-kauri a Nijeriya Hameed Ali, ya shaida wa ‘yan jarida a birnin tarayya Abuja cewa suna jiran umarni daga gwamnati a halin yanzu.

Kanal Hameed Ali (mai ritaya) ya bayyana cewa kowane lokaci daga yanzu (a jiya), takarda za ta iya fito wa daga ofishin Ministar tattalin arziki na kasa.

Jaridar Punch tace ana sa ran cewa a makon gobe ne ragin kudin harajin da gwamnatin tarayya ta yi wajen shigo da motoci daga kasar waje zai fara aiki.

Jama’ar Najeriya dai na cigaba da bayyana ra’ayoyin su dangay da wannan cigaba da aka samu, inda wasu ke ganin mataki ne wanda ya kamata tun tuni ace an yi.

A halin yanzu dai abin a jira a gani shine abin da zai biyo baya bayan ?aukar mataki da gwamnatin ta yi.

Related posts

Leave a Comment