Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya gana da sabbin shugabannin tsaro a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Abuja jiya Laraba, domin kara musu ?aimi akan babban ?alubalen da ke gabansu na samar da tsaro a Najeriya.
Shugaban ?asan ya yi kira ga sababbin hafsoshin tsaron bukatar su nuna kishin kasa, su jajirce tare da yin aiki da kyau, domin dawo da martabar tsaro wadda ta da?e da lalacewa a kasar.
Mai magana da yawun Shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar da jawabi bayan zaman da Buhari yayi da sabbin shugabannin tsaron.
Kamar yadda Garba Shehu ya bayyana, Ministan tsaro na kasa, Janar Bashir Magashi (mai ritaya) ne ya jagoranci hafsosy sojojin zuwa wajen shugaban kasa.
“Muna cikin wani mawuyacin yanayi. Ku nuna kishin kasa, ku yi wa kasa aiki, ita ku ke yi wa bauta.”
“Babu abin da zan iya fada maku domin a cikin wannan aiki ku ke. Ni ma ina ciki a da, kuma zan yi maku addu’a.” inji shugaban kasar.
“Ina so kuma in tabbatar maku da cewa zan yi duk abin da zan iya a matsayina, saboda mutane su yaba da kokarinku.” “Kun san halin da mu ke ciki a 2015, kun san yadda mu ke a yau, da irin nasarorin da mu ka samu.
Buhari ya ce ya yi alkawarin zai samar da tsaro a Najeriya, cikin alkawuran da shugaban kasar ya yi na kawo zaman lafiya, yaki da rashin gaskiya da farfado da tattalin arziki, ya ce aikin akwai wahala, amma ana nasara.
Janar Leo Irabor ya yi jawabi bayan taron a madadin sauran abokan aikinsa, ya ce Buhari ya fada masu cewa ana da sa ran za su yi kokari, don haka sai sun dage.
