Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa babban Bankin Najeriya, CBN, ya ?ara yawan ku?in ruwa da kashi 0.2 cikin 100 da masu cin bashi daga bankuna za su dinga biya a ?asar.
Hakan na nufin yanzu duk wanda ya ci bashin banki zai biya kashi 18.75 na ku?in da ya kar?a, maimakon 18.5 da aka saka a watan Mayu da ya gabata.
CBN ya ?auki matakin ne da zimmar da?ile hauhawar farashi ta hanyar rage wa mutane sha’awar mallakar zunzurutun ku?i.
Mu?addashin Gwamnan CBN Fola Shonubi ya ce bankin ya cimma wannan matsaya ce bayan la’akari da tasirin cire tallafin mai, da na ha?e kan kasuwar canjin ku?i, da kuma yun?urin gwamnati na rarraba kayan tallafi.
Wannan ne ?ari na farko da Shugaba Bola Tinubu ya yi bayan sauran matakan tattalin arziki da ya ?auka tun bayan hawansa mulki a watan Mayu.
