Ba Za Mu Lamunci Duk Wani Yunkurin Juyin Mulki A Afirka Ba – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya ce ?ungiyar raya tattalin arzi?in ?asashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ba za ta amince da abubuwan da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar ba.

Da safiyar yau Laraba ne rahotanni suka bayyana cewa dakarun tsaro sun toshe fadar shugaban ?asa da ofisoshin jami’an gwamnati a kasar.

A martanin da ya mayar a cikin wata sanarwa, Tinubu wanda shi ne Shugaban ECOWAS ya ce ba za a lamunci yun?urin juyin mulkin sojoji ba.

Sanarwar ta ce “Bayanan da aka samu daga jamhuriyar Nijar na nuni da wasu abubuwa marasa dadi da ke faruwa a ?angaren shugabannin siyasar ?asar.”

Related posts

Leave a Comment