Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki a ta gayyaci za?a??en shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu, tare da mataimakinsa Kashim Shettima, da sauran za?a??un sanatoci na ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar zuwa wata ganawa ta musamman.
An tsara gudanar da ganawar ranar Litinin a fadar gwamnati da ke Abuja babban birnin ?asar.
Rahotonni na cewa an tsara ganawar ne domin tattauna batun shugabancin majalisun dokokin ?asar biyu da yadda za a rarraba mu?aman majalisun zuwa shiyyoyin ?asar daban-daban.
Gayyatar ganawa da za?a??un wakilan – wadda sakataren jam’iyyar na ?asa, Iyiola Omisore ya sanya wa hannu aka kuma wallafa a shafin jam’iyyar na Twitter – ta bayyan cewa za a yi ganawar ne ranar Litinin 13 ga watan Maris da misalin ?arfe 12:00 na rana.
Jam’iyyar ta kuma bu?aci duka za?a??un wakilan su hallara tare da takardun shaidar cin za?e da hukumar za?en ?asar ta ba su.
Ganawar na zuwa ne bayan da tuni wasu ‘yan majalisun suka fara bayyana sha’awarsu ta zama shugabannin majalisun dokokin ?asar biyu.
Samun ha?in kan shugabancin majalisun biyu dai na da matu?ar tasiri wajen gudanar da ayyuka a ?angaren shugaban ?asa.
