Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar jigon jam’iyyar PDP, Sam Ohuabunwa ya bayyana cewa ya kamata shugabansu Iyorchia Ayu yayi murabus kan rikicin dan takarar shugaban kasa Atiku da gwamna Wike.
Sam Ohuabunwa ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da manema labarai na Channels,
A baya shugaban jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya bayyana cewa zai yi mirabus idan har jam’iyyar ta tsayar da dan takarar shugaban kasa daga arewacin Najeriya.
Saboda haka ya kamata ya cika alkawarin daya masu yayi murabus tunda ba dan kudu ne ya zamo dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ba, wanda hakan ne yasa har yanzu Atiku da Wike basa jitituwa a tsakaninsu.
