Rahoton dake shigo mana Jihar Anambra na bayyana cewar Sanata mai wakiltar maza?ar Anambra ta arewa a majalisar dattijai, Sanata Stella Oduah, tace, “Duk wanda yace Buhari ya watsar da Kudu maso Gabas, to baiwa kan shi adalci ba haka yankinsa.”
Sanata Oduah, bisa wakilcin Amaka Ononuju, ta fa?i haka ne a wurin taron sauya she?arta da ya gudana a sakateriyar APC dake Awka, baban birnin Jihar Anambra, dake sashin Kudu maso gabashin Najeriya.
A cewar sanatan, ta ?auki matakin ficewa daga PDP zuwa APC ne domin ta samu damar kawo dumbin ayyuka maza?arta daga gwamnatin tarayya.
“Babu adalci mutum yace shugaba Buhari da jam’iyyar APC ba su yi komai a yankin kudu maso gabas ba, wannan son rai ne.”
Hakanan kuma sanata Oduah ta yaba wa shugaban ?asa Muhammadu Buhari, bisa, “manyan ayyukan raya ?asa da gwamnatinsa ta yi a yankin kudu maso gabas.” Bugu da ?ari tace babu bukatar ?arin bayanai kan manyan ayyukan da gwamnatin APC ?ar?ashin shugaba Buhari ta yi a yankin kudu maso gabas domin kowa na gani.
Sanatan ta bayyana cewa kasancewar yanzun ta dawo jam’iyya mai mulki, zata maida hankali wajen ?aukar matakan da suka dace na cigaban ?asa. Oduah ta yi al?awarin marawa ?an takarar jam’iyyar APC, Andy Ubah, baya a za?en gwamnan jihar Anambra dake tafe.
