Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar sojin saman Najeriya ta musanta rahotannin da ake ya?awa a shafukan sada zumunta da ke zarginta da biyan ?an bindiga naira miliyan 20 don mi?a mata wata bindigar harbo jirgin ya?i.
Rahotannin da ake ya?awa sun ce an biya wasu ?an bindiga a yankin ?aramar hukumar Jibia a jihar Katsina ku?in ne don su bai wa rundunar bindigar, wadda suka ce rundunar na fargabar ?an bindigar na iya amfani da ita wurin harbo jiragen da ake aiki da su a jihar Katsina.
A sanarwar da ta fitar, rundunar sojin saman ta ce babu ?amshin gaskiya a rahotannin kuma an ?ir?ire su ne don a ?ata sunanta.
Ta yi kira ga mutane su yi watsi da labarin wanda ta ce na bogi ne.
Rundunar ta ce babu wani dalili da zai sa rundunar ta biya ?an bindiga ku?i a lokacin da take ci gaba da kai masu hari a jihar Katsina da wasu sassan yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Ta kuma bayyana cewa ranar 12 ga watan Oktoban 2021, rundunar ta ?addamar da hare-hare biyar a yankin Jibia da rokoki a wurin da jagoran ?an bindiga Bala Wuta da yaransa ke ayyukansu a Kadaoji.
Baya ga wannan ta ce ta kai hare-hare masu kama da shi a Fakai Dutsin Anfare.
