Filato: Gwamna Lalong Ne Ya Kamata Ya Gaji Buhari – APC

Rahotanni daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewar wasu shugabannin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Filato sun fara kulla-kulla don ganin gwamnan jihar, Simon Lalong ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Jiga-jigan jam’iyyar sun hadu a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, a Jos, babban birnin jihar, inda suka yanke shawarar marawa gwamnan baya kuma suka fara masa kamfen.

Jagoran tawagar, Alhaji Saleh Zazzaga, wanda ya yi magana a wurin taron ya ce Lalong ya cancanci tsayawa takara, lashe zaben da kuma samar da kyakkyawan shugabanci ga ‘yan Najeriya.

Ya bayyana yadda gwamnan ya “dinke bambancin kabilanci da addini” a tsakanin kungiyoyi daban-daban masu akida mabanbanta a jihar. “Saboda kyakkyawan shugabanci na Lalong, ya sa aka nada shi Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, wanda a kansa ya kasance mai gina gadar zaman lafiya, fahimta da ci gaban yankin arewa da kasa baki daya.

“Bugu da ?ari, duk da mawuyacin halin da tattalin arziki ?asar ke ciki da raguwar ku?a?en shiga a jihar, Lalong ya ci gaba da biyan albashin da ba a ta?a gani ba, yayin da sauran gwamnonin jihohi ba sa iya yin hakan.”

Related posts

Leave a Comment