‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Kazamin Hari A Jihar Kaduna

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne ?auke da muggan makamai sun kashe mutum hudu a wani kauye ciki har da wani sabon malami a karamar hukumar Kajuru dake jihar ta Kaduna.

Harin ya yi sanadin rayuka uku ciki har da wani shugaban matasa a daren ranar Lahadi. Mazaunin garin ya yi ?arin haske kan harin Within Nigeria ta tattaro cewa a harin na biyu a Tudun Mare ne aka kashe wani malami mai suna Elisha Arziki.

Wani mazaunin garin mai suna Benjamin, ya ce: “Yan bindigan sun kashe shugaban matasan da wasu mazauna kauyen biyu lokacin da suka kawo hari a ranar Lahadi. An birne su a ranar Lahadi. Yan bindigan kuma sun kashe wani malami a kauyen Tudun Mare a daren ranar Litinin.”

Kakakin yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya yi alkawarin zai kira Wakilinmu ya bada karin bayani amma bai kira ba har lokacin hada wannan rahoton.

Related posts

Leave a Comment