Fatali Da Bukatun Mata A Siyasa: Kungiyoyin Mata Sun Yi Zanga-Zanga

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?aruruwan mata a karkashin kungiyoyi kamar su Action Aid, da WRAPA mai nema wa mata ‘yancinsu, da kungiyar WIMBIZ mai taimaka wa mata masu sana’a da dai sauransu ne suka fito zanga zangar lumana domin neman ‘yan Majalisar dokokin Najeriya su sake nazari akan matakan da suka dauka na yin watsi da kudurin ba mata damar shiga cikin sha’anin tafiyar da kasa.

Kungiyoyin Matan sun ?ara da cewa ba su san inda aka sami matsala ba saboda tun farko mazan sun nuna musu goyon baya dari bisa dari kafin daga bisani suka yi fatali da bukatun nasu.

Ene Obi, da ke zaman babbar wakiliya a kungiyar Action Aid a Najeriya, ta bayyana cewa ya zama wajibi ‘yan Majalisar su sake nazari su zartar da kudurin ya zama doka don ba mata damar wakilcin da ya kamata.

‘Yar majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Isuikwato/Ummunneochi, Nkiruka Onyejocha, ta fito rarrashin ‘yan uwanta mata da su yi hakuri su koma gida a daura damarar sake nazari don fito da sabbin dabarun da zasu taimaka wajen shawo kan maza su ba su hakkinsu.

Ita ma tsohuwar ministar ayyukan mata Malama Aisha Isma’il ta bayyana rashin jin dadinta kan wannan batu.

A ranar Talata ne dai Majalisar dokokin ta yi watsi da kudurin nema wa mata kaso 35 a bangaren samun mukaman siyasa don su taimaka wa ‘yan uwansu da kuma neman ci gaban kasa.

Related posts

Leave a Comment